エピソード

  • Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe
    2025/10/09

    Send us a text

    A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci.


    Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya da amana.


    wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Tasirin Takardun Shaida Na Bogi Ga Rayuwar Al’umma
    2025/10/07

    Send us a text

    Takardun shaida na bogi na daya daga cikin matsaloli dake kara addabar Najeriya a fannoni da dama.


    A wasu lokuta ana samun mutane da ke amfani da takardun makaranta ko na ƙwarewa da ba su cancanta da su ba domin samun aiki, mukami, ko wasu fa’idodi da suka wajaba ne kawai ga waɗanda suka cancanta.

    Wannan dabi’a ta zama barazana ga ci gaban ƙasa da amincin al’umma gaba ɗaya, domin tana lalata tsarin ilimi, rage darajar masu gaskiya, da haifar da rashin inganci a wuraren aiki. Haka kuma, tana haifar da rashin amincewa tsakanin gwamnati da jama’a, da kuma tsakanin mutane da kansu.


    wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • ‘Halin Kunci Ya Sa Muke Zama A Baca A Abuja’
    2025/10/06

    Send us a text

    Halin matsin tattalin arziki ya tilasta da yawa daga cikin mutane zama a bacoci a garin Abuja da wasu biranen Najeriya.


    Mutane a birane kamar Abuja da Legas Da Fatakwal na cikin halin matsi sakamakon rashin ingattaccen muhalli.

    Ko wannen irin rayuwa irin wadannan mutanen ke yi?


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai a yau da ake bikin ranar muhalli ta duniya.

    続きを読む 一部表示
    27 分
  • Yadda Fasahar AI Ke Barazana Ga Sana’ar Masu Shagunan Daukar Hoto
    2025/10/03

    Send us a text

    A zamanin yau na fasahar zamani, musamman fasahar kirkirarriyar basir ta (AI), harkokin sana’o’i da dama suna fuskantar sauye-sauye masu girma. Daya daga cikin sana’o’in da ke cikin babban hadari shi ne sana’ar ɗaukar hoto musamman irin wadanda ke kashe makudan kudi wajen sayen kyamara da bude katafaren gidajen daukar hoto.


    A da, mutane kan je shagon daukar hoto domin samun hoto mai kyau na fasfo ko na bikin aure ko bikin suna, ko kuma kowane irin taron biki. Amma yanzu, manhajojin AI suna ba wa mutane damar kirkirar irin wadannan hotuna daga wayoyin su ko kwamfuta cikin mintuna kadan ba tare da zuwa shagon daukar hoto ba.

    Wannan yanayi na iya jefa masu shagunan daukar hoto cikin matsala ta rashin samun kudin shiga da kuma rasa sana’ar gaba ɗaya, muddin ba su bullo da sabbin dabarun jawo hankalin kwastomomi ba.


    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.

    続きを読む 一部表示
    23 分
  • Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Takarar Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan
    2025/10/02

    Send us a text

    Batun siyasar Najeriya ya sake ɗaukar hankali yayin da jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa a 2027.
    Wannan batu ya tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masana, da ‘yan siyasa da ma al’umma.


    Idan za a iya tunawa dai, an rantsar da tsohon shugaban ƙasan, har sau biyu: a karo na farko a shekarar 2010 bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua, sannan kuma a karo na biyu a 2011 bayan lashe zaben da ya biyo baya.

    Amma abun tambayar a nan shine, shin ko me dokar kasa ta bayyana kan takarar tsohon shugaban kasan bayan rantsar dashi har sau biyu kan karagar mulki?
    Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.


    wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.

    続きを読む 一部表示
    27 分
  • Me Ya Sa Mutane Suka Dawo Daga Rakiyar Kirifto?
    2025/09/30

    Send us a text

    A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto.

    Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar.

    Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto.

    続きを読む 一部表示
    26 分
  • Hanyoyin Da Dangote, PENGASSAN Ba Su Bi Ba Don Magance Takaddamarsu
    2025/09/29

    Send us a text

    Gwamnatin Tarayya ta gayyaci Kungiyar Manyan Ma’aikatan Man Fetur da Iskar Gas ta Najeriya (PENGASSAN) da Matatar Dangote don a sasanta a yau.


    Hakan ya biyo bayan umarnin da ’yan kwadagon suka bai wa mambobinsu ne na shiga yajin aiki bayan da Matatar Dangote ta salami ma’aikata fiye da 800.

    Sai dai wasu masana suna ganin tun farko bai kamata lamarin ya kai ga haka ba da an bi wasu hanyoyi.


    Wadannan hanyoyi shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai binciko.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Hanyoyin Magance Gubar Cikin Abinci
    2025/09/26

    Send us a text

    Cin guba ta hanyar abinci (food poisoning) wata cuta ce da ke faruwa idan mutum ya ci abinci ko ya sha abin sha da ya gurɓace. Gurɓacewar abincin na iya fitowa daga ƙwayoyin cuta kamar Salmonella, E. coli, ko Listeria, ko kuma daga ƙwayoyin cutar virus, ƙwari (parasites), ko sinadarai masu guba.


    Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, amai, zazzabi, gudawa, da rashin jin daɗin jiki. A wasu lokuta masu tsanani, cutar na iya kai mutum asibiti ko ta yi barazana ga rayuwa, musamman ga yara ƙanana, mata masu ciki, tsofaffi, da masu raunin garkuwar jiki.


    wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba akai.

    続きを読む 一部表示
    26 分