Yadda Siyasar Ubangida Ta Yi Tasiri Ga Siyasar Najeriya A Jamhuriya Ta Hudu
カートのアイテムが多すぎます
カートに追加できませんでした。
ウィッシュリストに追加できませんでした。
ほしい物リストの削除に失敗しました。
ポッドキャストのフォローに失敗しました
ポッドキャストのフォロー解除に失敗しました
-
ナレーター:
-
著者:
概要
Send us a text
Tun bayan dawowar mulkin farar hula a shekarar 1999, siyasar Najeriya ta kasance karkashin inuwar wasu ’yan tsiraru da ake kira iyayen gidan siyasa. Wannan tsari ya ginu ne a kan karfin mutum guda ko rukuni, inda su ke rike da makullin jam’iyya, su tsara wa’adi, su zabi ’yan takara, su kuma yanke hukunci ba tare da la’akari da ra’ayin mafi yawan mambobi ko jama’a ba.
A Jamhuriya ta Hudu, siyasar ubangida ta zama tamkar al’ada da aka amince da ita, inda dimokuraɗiyya ta hakika ke fuskantar barazana daga siyasar biyayya da ladar mukami. A maimakon gasa ta tunani, da tsari da manufofi, an koma fafatawa ta kusanci da ubangida, wanda hakan ya raunana jam’iyyu, ya haifar da rikice-rikicen cikin gida, tare da jefa talakawa cikin rashin tabbas game da sahihancin zabensu.
A cigaba da kawo muku shirye shirye gabanin Muhawarar Daily Trust ta 2025, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan Siyasar Uban gida ya yi tasiri da kuma yadda ya juya akalan siyasar Najeriya tun dawowar jamhuriya ta hudu a Najeriya.