Tasirin Siyasar Matasa A Najeriya Tun Bayan Dawowar Jamhuriya Ta Hudu
カートのアイテムが多すぎます
カートに追加できませんでした。
ウィッシュリストに追加できませんでした。
ほしい物リストの削除に失敗しました。
ポッドキャストのフォローに失敗しました
ポッドキャストのフォロー解除に失敗しました
-
ナレーター:
-
著者:
概要
Send us a text
Shekaru kafin a sanya hannu kan dokar Not Too Young To Run, siyasar matasa a Najeriya na fuskantar ƙalubale masu tarin yawa. Duk da cewa matasa su ne mafi rinjaye a yawan al’umma da kuma masu katin zaɓe, an dade ana kallonsu ne a matsayin masu ɗaukar tutoci, da yaɗa saƙonni ko kuma masu tayar da tarzoma a lokacin zaɓe, ba tare da ba su cikakkiyar dama ta tsayawa takara ko shiga manyan matakan yanke shawara ba.
Sai dai a shekarar 2018, bayan sa hannu kan dokar bai wa matasa dama a siyasar Najeriya, an samu sabon salo da fata a fagen siyasa. Dokar ta rage shekarun tsayawa takara a muƙaman siyasa daban-daban, tare da buɗe ƙofa ga matasa masu ƙwazo, da ilimi da kishin ƙasa su shiga fafutukar jagoranci kai tsaye. Wannan mataki ya ƙarfafa gwiwar matasa da dama su fara ganin siyasa a matsayin fagen da za su iya kawo sauyi, ba wai kawai a matsayin masu goyon baya ba.-
A cigaba da kawo muku shirye gabanin muhawarar Daily Trust, shirin Njaeriya a yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan ko yadda siyasar matasa ta kasance a jamhuriya ta hudu tun bayan ayyana wannan doka.