Zabukan Da Aka Gudanar Lokacin Dawowar Mulkin Farar Hula A Jamhuriya Ta Hudu
カートのアイテムが多すぎます
カートに追加できませんでした。
ウィッシュリストに追加できませんでした。
ほしい物リストの削除に失敗しました。
ポッドキャストのフォローに失敗しました
ポッドキャストのフォロー解除に失敗しました
-
ナレーター:
-
著者:
概要
Send us a text
Bayan kusan shekaru goma sha shida na mulkin soja, Najeriya ta dawo kan tafarkin mulkin farar hula a shekarar 1999, abin da ya buɗe sabon babi a tarihin siyasar ƙasar. Zaɓen da aka gudanar a wannan lokaci shi ne zaɓen farko na Jamhuriya ta Huɗu, inda aka gudanar da zaɓukan kananan hukumomi, majalisun dokoki, gwamnoni da kuma shugaban ƙasa a ƙarƙashin kulawar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, wato INEC.
Duk da cike da ƙalubale kamar ƙarancin kayan aiki, rashin cikakken shiri, zarge-zargen maguɗin zaɓe da kuma ƙarancin wayar da kan jama’a, zaɓen ya kasance muhimmin mataki na dawo da ikon mulki hannun farar hula. Jama’a da dama sun shiga zaɓen ne da fatan ganin ƙarshen mulkin soja da kafa gwamnati mai wakiltar ra’ayin al’umma.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi waiwaye ne kan zabukan farko da aka gudanar a jamhuriya ta hudu bayan dawowar mulkin farar hula a Najeriya.