Abun Koyin ‘Yan Siyasa Da Matasa Kan Jarumtar Goodluck Jonathan A 2015
カートのアイテムが多すぎます
カートに追加できませんでした。
ウィッシュリストに追加できませんでした。
ほしい物リストの削除に失敗しました。
ポッドキャストのフォローに失敗しました
ポッドキャストのフォロー解除に失敗しました
-
ナレーター:
-
著者:
概要
Send us a text
Kiran wayan da tsohon Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya yi wa marigayi Muhammadu Buhari ta bar tarihi mai muhimmanci a Najeriya.
Waya da ta kwantar da hankalin kasa, ta kuma dakatar da fargabar tashin hankali.
A ranar da sakamakon zaben shekarar 2015 ya fara bayyana, tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya zabi zaman lafiya a kan mulki, ya kuma zabi Najeriya a kan kansa.
Maimakon ya tada jijiyar wuya, ko ya kalubalanci sakamakon da zai iya haddasa rikici, Goodluck Jonathan ya dauki waya, ya kira abokin takararsa, tsohon shugaban kasa Marigayi Muhammadu Buhari, ya taya shi murnar nasara. Wannan mataki ya nuna jarumtaka, da kishin kasa, da girmama dimokuraɗiyya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan bajintar da tsohon shugaban kasa Goodluck jonathan ya nuna a tarihin Najeriya.