Nasarori Da Kalubalen Da Bankin Musulunci ke Fuskanta A Najeriya
カートのアイテムが多すぎます
カートに追加できませんでした。
ウィッシュリストに追加できませんでした。
ほしい物リストの削除に失敗しました。
ポッドキャストのフォローに失敗しました
ポッドキャストのフォロー解除に失敗しました
-
ナレーター:
-
著者:
概要
Send us a text
A Jamhuriya ta Hudu a Najeriya, wadda ta fara a shekarar 1999, an samu sauye-sauye masu yawa a bangaren tattalin arziki da harkokin kuɗi, ciki har da tasowar bankunan Musulunci. Wannan tsari na banki ya samo asali ne daga buƙatar samar da hanyoyin mu’amala da kuɗi da suka dace da koyarwar addinin Musulunci, wato hanyoyin da ba su ƙunshi riba, da zamba, ko rashin tabbas ba.
A farkon lokaci, ra’ayin kafa bankunan Musulunci ya fuskanci muhawara da adawa daga wasu ɓangarori na al’umma, musamman saboda fahimtar da ake yi cewa tsarin na da alaƙa da addini. Sai dai daga bisani, gwamnati da hukumomin kula da harkokin banki, musamman Babban Bankin Najeriya (CBN), sun samar da dokoki da ka’idoji da suka bai wa bankunan Musulunci damar aiki a matsayin bankunan da basa cin riba.
A cigaba da kawo muku shirye shirye gabanin muhawarar Daily Trust, shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne akan tasowar bankunan musulunci da kalubalen da suke fuskanta.