エピソード

  • Shin Ko Zafin Nema Na Kawo Samu?
    2025/07/09

    Mai yiwuwa masu sauraro sun san wani bawan Allah wanda kusan a kullum, kuksan a ko yaushe a cikin nema yake, amma Allah bai kawo ba..


    Wasu dai na ganin yawan fadi-tashin da mutum yakan yi ba shi ne zai ba shi kudaden da yake bukata ba, yayin da wasu suke ganin jajircewar mutum tana da nasaba da yawan abin da zai samu.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan kujiba-kujibar da mutane suke yi don samun arziki da tambayar ko zafin nema yana kawo samu?

    続きを読む 一部表示
    19 分
  • Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa
    2025/07/02

    Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare.


    A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin hali.


    Shirin Najeriya A Yau na wannan makon zai yi nazari ne kan sinadaran da ake amfani da su wajen sarrafa burodi da kuma irin cutar da suke jawowa.

    続きを読む 一部表示
    29 分
  • Shin Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
    2025/06/18

    Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya.


    Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya.

    Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya.

    Kazalika a kwanakin nan wani hari da aka kai a wasu yankunan jihar Binuwe yayi sanadiyyar halakar mutane da dama, wadda hakan ya jawo cece ku ce da ya kai har wasu na kiran mutane su tashi don kare kan su.

    Irin wannan kira dai an dade ana yi, sai dai gwamnati na ganin ba daidai ne mutane su kare kan su daga hare haren ‘yan ta’adda ba.


    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan shin ko kare kai daga hare haren ‘yan ta’adda zai kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya?

    続きを読む 一部表示
    29 分
  • June 12: Me Ranar Demokradiyya Ke Nufi Ga Talakan Najeriya?
    2025/06/12

    An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi.


    Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.


    Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

    続きを読む 一部表示
    28 分
  • Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami'an Kiwon Lafiya
    2025/06/11

    Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso.


    Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa.
    A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jami’an lafiya.
    Sai dai ’yan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jami’an kiwon lafiya kan nuna halin ko-in-kula, a wasu lokutan ma da sakaci, wanda kan kai rasa rayuka.


    Shirin Daga Laraba na wannan mako zai zube komai a faifai don gano sahihancin wannan zargi da ’yan Najeriya suke yi da kuma, idan zargin ya tabbata, yadda aikin jami’an lafiya ya yi hannun riga da abin da aka karantar da su.

    続きを読む 一部表示
    26 分
  • Dalilan Tashin Farashin Kayan Miya Gabanin Bikin Sallah
    2025/06/04

    Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah.


    Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan wannan batu.


    shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa farashin kayan miya suka yi tashin gwauron zabo gabanin bikin Sallah.

    続きを読む 一部表示
    26 分
  • “Sai Na Tara Kudin Cin Abinci Na Nake Iya Siyan Audugar Al’ada”
    2025/05/28

    Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli.


    A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace ‘yan mata goma a ƙasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa makaranta lokacin da take jinin al’ada, saboda rashin kayan tsafta, ruwa da kuma tsaftatattun ban daki.

    Irin wannan matsala na addaban mata marasa galihu da wadanda ke zama a karkara.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan irin matsalolin da mata ke fuskanta yayin jinin al’adar su.

    続きを読む 一部表示
    24 分
  • "Abba Al'mustafa Bashi Da Hurumin Dakatar Da Fina Finan Mu"
    2025/05/21

    Dangantaka na kara runcabewa tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano, wato Kano State Censorship Board, hukumar da aka kafa a shekarar 2001 domin kula da tsaftar fina-finai da nishaɗi a jihar, musamman a fannin kiyaye al’ada da koyarwar addini wacce daya daga cikin jaruman fina finan Abba El-Mustapha, ke jagoranta.


    A baya-bayan nan, hukumar ta fitar da sanarwa inda ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22. Wannan mataki ya biyo bayan saɓani tsakanin hukumar da wasu masu shirya fina-finai, inda hukumar ke zargin cewa fina-finan sun ƙetare ƙa’idoji.
    Sai dai masu shirya fina finan sun bayyana cewa sam hukumar bata da hurumin dakatar da wadannan finafinai.


    Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan rigimar da ta balle tsakanin hukumar tace fina finai ta jihar Kano da kuma masu shirya fina finai masu dogon zango.

    続きを読む 一部表示
    27 分